Wani zama na sasanci tsakanin Majalisar Shura ta Jihar Kano da malamin addini, Malam Lawal Abubakar Triumph, ya gudana a ofishin Hukumar Tsaro ta DSS da ke Kano a ranar Litinin.
An gudanar da taron ne ƙofa rufe, inda mambobin Majalisar suka shawarci malamin da ya riƙa yin taka-tsantsan da natsuwa a cikin bayanansa na addini. Rahotanni sun nuna cewa malamin ya nemi afuwa a yayin tattaunawar.
- Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
- Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura
Bayan kammala zaman, Malam Lawal Triumph ya wallafa kalmar “Alhamdulillah” a shafinsa na Facebook abin da jama’a da dama suka fassara a matsayin alamar cewa an kammala sasanci lafiya tsakaninsa da Majalisar Shura.
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito a baya cewa Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa lamarin ga Majalisar Shura domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Malam Triumph na yin kalaman batanci a cikin wani wa’azi da ya yi, wanda ya jawo cece-kuce da ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban na al’umma.
Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana.