Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin.
Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda zai iya tsoratar da mu,” in ji shi.
- Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi
- ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta
Shugaban ASUU ya kuma shawarci Ministan Ilimi da ya maida hankali wajen warware rikicin maimakon yin barazana. “Ya kamata ya karkata kan magance wannan matsalar. Idan kuma ya ci gaba da bin wannan hanyar ta barazana, zai gaza,” Piwuna ya ƙara da cewa.
Duk da matsayinta mai tsauri, ASUU ta bayyana cewa tana shirye don tattaunawa da gwamnati. Piwuna ya ce sun samu kiran Ministar Ƙwadago, wadda ta bayyana cewa an umurce ta da shiga tsakani don warware rikicin. “ASUU a shirye take, muna son tattaunawa don kawo ƙarshen wannan ƙwan gaba ƙwan baya,” in ji shi.