Kafofin watsa labarun kasashen waje sun yaba da taron kolin mata na duniya da aka bude a birnin Beijing a jiya Litinin 13 ga watan nan na Oktoba. Kafofin sun ce, “Wannan taron yana da matukar muhimmanci, yana kara ciyar da daidaiton jinsi, da cikakken ci gaban mata a duniya gaba.”
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron a jiya, ya kuma gabatar da jawabi, inda ya ba da shawarwari hudu na hanzarta sabon tsarin cikakken ci gaban mata, sannan ya sanar da matakai biyar da Sin za ta dauka don tallafawa ci gaban mata a duniya.
Shugabannin da suka halarci taron sun yi imanin cewa, yayin da Sin ke samun nasarar ci gaban mata a cikin gida, ta kuma nuna aniyar sauke nauyi, da jagoranci mai karfi a fannin shigar da kuzari ga ci gaban mata a duniya.
A halin yanzu, sama da mata da yarinya miliyan 600 a duniya suna cikin rikici da yaki, sannan mata da ‘yan mata biliyan 2 ba su da tabbacin tsaron zamantakewa. Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana, cewar har yanzu ci gaban mata a duniya yana fuskantar “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba”, kasashe suna bukatar kuduri da hikima don magance matsalolin mata. A lokacin kaka na shekara ta 2025, daga Beijing za a sake samun ci gaba, wato Sin tana fatan ta kara hada kai da sauran bangarori, don hanzarta cikakken ci gaban mata, da kuma ba da gudummawar mata don ciyar da ci gaban bil’adama gaba. (Amina Xu)














