Sashen cinikayyar kamfanonin sarrafa hajoji na kasar Sin ya samu ci gaban kaso 4.7 bisa dari a mizanin shekara-shekara, a rubu’i uku na farkon shekarar nan ta 2025. Ci gaban sashen ya shaida karuwar kaso 29.8 bisa dari na jimillar kudaden shiga daga kayayyakin da kamfanonin suka sayar.
Bayanan da hukumar tattara haraji ta kasar ko STA ta fitar dangane da hakan, sun nuna yadda kyawawan manufofi irinsu rangwamen haraji, da rage kudaden hidima da kamfanonin suke biya suka taimaka matuka wajen cimma wannan nasara.
Hukumar ta STA, ta kara da cewa Sin na samun ci gaba a fannin inganta ayyukan sarrafa hajojin masana’antu, da amfani da na’urorin zamani, da masu kare muhallin halittu, da samar da muhimmin goyon baya ga ci gaban tattalin arziki. (Saminu Alhassan)