Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya soki Gwamna Douye Diri da sauran mambobin jam’iyyar PDP da suka sauya sheƙa, inda ya ce suna tsere wa matsalolin da suka haifar da kansu a jam’iyyar.
Yayin da yake magana bayan zaman Majalisar Dattawa a ranar Laraba, Dickson ya ce Diri ya tattauna da shi sau da dama kan shirin barin PDP, amma bai ga dalili mai ƙarfi ba da zai sa gwamna ya bar jam’iyyar da ta ɗora shi a kan mulki ba.
- Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
- Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar
Ya ce Najeriya tana buƙatar dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama, ba jam’iyya ɗaya tilo da ke haifar da mulkin kama-karya ba.
Ya ƙara da cewa: “Ni ina nan a PDP, kuma ina goyon bayan dimokuraɗiyya mai ƙarfi da jam’iyyu da dama, ba irin ta jam’iyya ɗaya ba.”
Dickson ya zargi wasu gwamnonin da shugabannin jam’iyyar PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar sannan suka zaɓi tserewa maimakon gyarawa.
Game da siyasar Bayelsa, ya ce bai taɓa taka rawa a matsayin uban gidan Diri ba, sai dai kawai yana ba da shawara idan aka nemi ra’ayinsa.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC).
“A matsayinsa na Farfesa a fannin shari’a kuma SAN na farko da aka naɗa a wannan matsayi, ya fahimci nauyin da ke kansa. Zan goyi bayan tabbatar da naɗinsa,” in ji Dickson.