A yau Jumma’a ne ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta fitar da rahoto game da biyayyar Amurka ga ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO na shekarar nan ta 2025.
Jami’i mai lura da sashen cinikayyar kasa da kasa a ma’aikatar, ya bayyana cewa, yanayin da ake ciki yanzu haka dangane da tsarin cinikayyar mabambantan sassa na fuskantar tarin halubale. A nata bangare kuwa, kasar Sin na kira ga Amurka da ta gyara kura-kuranta kan lokaci, ta kuma martaba ka’idojin WTO, ta kuma sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na memba a kungiyar, kana ta gaggauta yin watsi da matakan karya doka irinsu kakaba “harajin ramuwa”, ta hanyar fitar da rahoton shekarar 2025. Bugu da kari, ta mara baya ga tsarin cinikayyar mabambantan sassa, ta yadda hakan zai taka rawar gani ga jagorancin duniya, tare da aiki tukuru don cimma nasarar kare tsarin tasirin mabambantan sassan duniya, bisa daidaito da kyakkyawan tsari, da kuma kafa dunkulallen tsarin tattalin arzikin duniya, tare da sauran membobi ciki har da kasar Sin.
Tun daga shekarar 2023, bisa la’akari da nauyin dake wuyan Amurka a karkashin dokokin WTO, Sin ta ci gaba da fitar da rahoton biyayyar Amurka ga ka’idojin WTO, tana mai nuna damuwa game da matakan da Amurkan ke aiwatarwa, irinsu yunkurin dakile tsarin cudanyar cinikayya tsakanin mabambantan sassa, da cin zali irin na cinikayya, da yin baki biyu a fannin aiwatar da manufofin gudanar da masana’antu, da karan-tsaye ga tsarin sarrafawa da shigar da hajojin masana’antu sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)