A ci gaba da kokarin sake farfado da harkokin ilimi tare da karfafa gwiwar jama’a wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a yankunan da rikicin Boko Haram ya tagayyra tare da samar da zaman lafiya ga al’umma, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci Kasuwar Cross-Kauwa wadda a da sansanin ce ga mayakan Boko Haram a karamar hukumar Kukawa a arewacin Jihar Borno.
Gwamna Zulum ya shigar da ‘ya’yan ‘yan gudun hijira da marayun da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu kimanin 7000 zuwa makarantun Boko a garin Monguno.
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
- A KUSKURA: Yadda Kayan Maye Ya Zama Ruwan Dare A Tsakanin Al’umma
Ya ce gwamnatinsa tana da kyakkyawan shirin fadada shigar da yara makarantun, wanda rajistar zai tashi daga 7000 zuwa 10,000 nan gaba.
Gwamnan ya tabbatar wa da al’ummar yankin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ya dace domin ganin an samu zaman lafiya a yankunan tare da shan alwashin sake bude kasuwanni idan abubuwa suka kyautata.
Har ila yau, Gwamna Zulum ya jaddada cewa samar da abin dogaro da kai ga jama’a shi ne babban makami mai inganci wajen dakile duk wani yunkurin masu tayar da kayar baya.
Ya ce zama a sansanonin ‘yan gudun hijira ba shi da wata ma’ana, don haka a tallafa wa mutane domin su samu abin dogaro da kai shi ne ya fi dacewa.
Gwamnan ya yaba wa kokarin gwamnatin tarayya a karkashin Shugaban kasa Muhammdu Buhari da kuma rundunar sojojin Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki wadanda suka bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya a Jihar Borno.