Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da dake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake Alkaki:
Alkaki na daya daga cikin kayan zaki na gargajiyar Hausawa da ake ci sosai musamman a lokutan biki, Sallah, ko liyafa.
Ga dai yadda ake yin Alkaki a saukake
Abubuwan da ake bukata:
Garin Alkama (Flour), Kofi 3, Sukari Kofi 1, Man Gyada (Don Soya), Yis (Yeast) – Cokali 1,Ruwa dumi rabin kofi, Gishiri kadan, Madarar ruwa (ba dole ba)
Zuma ko syrup (domin jiko bayan an soya) idan ana so.
Yadda ake hadawa:
Da farko za a samu kwano a zuba ruwan dumi sannan a saka yis da dan sukari sai a barshi kamar minti 5 zuwa 10 don ya kumburo.
Sannan sai a samu wani kwano ko roba a zuba garin alkama da sukari da gishiri kadan sannan a zuba wannan hadin na yis da aka yi cikin garin, idan ana so za a iya zuba madara kadan saboda karin dandano.
Sannan sai a gauraya kullin sosai har sai ya yi laushi sannan kuma ba ya mannewa hannu, idan kuma ya yi tauri sai a dan kara ruwa kadan. Daga nan sai a rufe kullun abar shi a ajiye na kusan awa daya ya tashi domin yis din ya yi aiki kuma kullun ya narke.
Yadda za a nade shi:
Bayan ya tashi, sai a murza kullun a saman tebur, a yanka shi da wuka ko a yi masa siffofi kamar zobba, ko zare.
Sannan a zuba mai a abin suya a dora a wuta idan ya yi zafi sosai, sai a soya Alkakin har ya zama ruwan kasa-kasa (golden brown). A juya shi lokaci-lokaci domin ya yi daidai a kowane gefe.
Yadda za a jika shi:
Jiko da zuma ko Syrup:
Bayan an soya, sai a juye Alkaki din cikin zuma ko hadin syrup (sukari da ruwa da dan lemun tsami) don ya zama mai dandano da dan dandanon zaki.
Bayan ya huce kadan, sai a ci shi tare da shayi, nono, ko ruwa mai sanyi.
Alkaki na iya daukar kwanaki 2–3 ba tare da ya lalace ba idan an ajiye shi a busasshen wuri.














