Muƙaddashin shugaban hukumar daidaiton rabon muƙamai ta Ƙasa (FCC), Hon. Kayode Oladele, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ya samu kashi 56.3 cikin 100 na muƙamang gwamnatin tarayya da aka naɗa ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da Kudu ke da kashi 43.7 cikin 100.
Oladele ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron bita na kwana guda kan “Ƙarfafa Jagoranci da Gudanarwa Bisa Renewed Hope Agenda.” Ya ce wannan rabon yana nuna ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da adalci da daidaiton wakilci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
- DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki
- Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
A cewarsa, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma suna da ministoci mafi yawa, mutane 11 kowannensu, yayin da Arewa ta Tsakiya ke da 8, Arewa maso Gabas 7, Kudu maso Kudu 6, da Kudu maso Gabas 5. Bugu da ƙari, Arewa maso Yamma ce ke da yawan muƙaman jagoranci mafi girma (157), sai Arewa ta Tsakiya 139, da Kudu maso Yamma 132.
Oladele ya ce ko da yake Arewa ke da rinjaye a lissafi, hakan na nuna ƙoƙarin gwamnati wajen haɗa yankuna cikin tsarin daidaito, ba nuna wariya ba. Ya ƙara da cewa tsarin Federal Character ba kason mukamai ba ne, amma kayan aiki ne na haɗa kan ƙasa da tabbatar da wakilci na gaskiya.
Ya tabbatar cewa hukumar FCC za ta ci gaba da bibiyar sabbin naɗe-naɗe don tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun samu wakilci bisa Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu.