Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta samu nasara a karo na biyu a gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL) bayan ta doke abokiyar hamayyarta Kano Pillars da ci 2–1 a wasan da suka buga a yau Lahadi a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata, Kano.
Rabiu Ali, kyaftin ɗin Kano Pillars, ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Barau FC a minti na 20 da fara wasa. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ibrahim ya farke ƙwallon ga Barau FC a minti na 50, sai kuma Stanley da ya ƙara ta biyu wanda ya tabbatar wa Barau FC nasara a wasan.
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
- Kocin Kano Pillars Usman Abdullahi Ya Ajiye Aikinsa
Ko da yake Barau FC ta samu nasara a wasan na yau, hakan bai hana ta komawa matsayi na 18 a teburin gasar Firimiya ba, yayin da Kano Pillars ta cigaba da zama a matsayi na 20.
Pillars na da maki 5 kacal daga wasanni 8 da ta buga a bana, yayin da Barau FC ke da maki 8 daga wasanni 8 — inda ta ci wasa biyu, aka doke ta sau biyu, sannan ta tashi canjaras a wasanni biyu. Wannan kuma ita ce shekara ta farko da Barau FC ke buga gasar Firimiya ta Nijeriya.