Rundunar ‘yansandan jihar Delta ta ce ta kama alburusai 400 a babbar gadar, Asaba, babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Asaba, ya bayyana cewa, rundunar a karkashin jagorancin kwamishinan ‘yansandan, Olufemi Abaniwonda, na ci gaba da gudanar da ayyukanta na yaki da masu aikata laifuka a fadin jihar.
- Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu
- Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi
Ya ci gaba da cewa, “Ta hanyar amfani da kwarewa da kaifin basira, jami’an rundunar sun samu gagarumar nasara a yaki da miyagun kwayoyi da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
“Rundunar ‘yansandan sashi ‘C’, Asaba, karkashin jagorancin CSP Ogbe Emmanuel, sun samu nasarar tare wata mota ɗauke da alburusai da aka nufi jihar Edo da su.
“A yayin da jami’an suke gudanar da binciken motoci na yau da kullum a kan babbar gadar Asaba, jami’an sun yi nasarar tare wata mota kirar ‘Toyota Hiace Hummer Bus’ mai lamba NGK 16 XB, wacce wani Ozoemenam Sylvanus ke tukawa.
“Yadda Direban, ke amsa tambayoyi cikin rashin nutsuwa, ya jawo jami’an suka fahimci cewa, ba shi da gaskiya inda suka gudanar da bincike sosai a kan motar, inda aka gano alburusai 400 da aka ɓoye a cikin motar.
“Wanda ake zargin da farko ya yi karyar cewa makullai ne aciki, amma sai aka ga alburusai bayan bude jakar, nan take aka kama shi, tare da haramtattun kayan da ya ɗauko.”