Wani iftila’i ya afku da sanyin safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Hong Kong lokacin da wani jirgin saman dakon kaya na Emirates mai lamba EK9788 ya kauce hanyar titin jirgin ya afka cikin teku, inda ya bi takan motar wasu ma’aikatan filin jirgin biyu, kuma nan take suka mutu.
Rahotanni sun ce jirgin Boeing 747, wanda ya taso daga Dubai, ya kauce hanya ne da misalin karfe 3:50 na safe agogon kasar (7:50 na yamma agogon GMT) a lokacin da ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama. A cikin wani mummunan yanayi, jirgin ya yi karo da wata motar sintiri a filin jirgin da ke kusa da wurin kafin ya afka cikin tekun da ke bayan filin jiragen.
A cewar hukumomin filin jirgin saman, mutanen biyu da ke cikin motar sintirin, sun mutu nan take. Jami’an agajin gaggawa sun kaddamar da aikin ceto, inda suka yi nasarar ceto ma’aikatan jirgin guda hudu da ke cikin jirgin, wadanda suka tsira da rayukansu da kananan raunuka.