A daren Lahadi a ƙasar Chile, ƙasar Morocco ta kafa tarihi bayan da ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na ƴan ƙasa da shekaru 20, wanda hakan ya bai wa ƙasar damar lashe wannan kofi a karon farko a tarihin ta.
Yassir Zabiri, wanda ke taka leda a ƙungiyar FC Famalicao ta ƙasar Portugal, shi ne gwarzon wasan bayan da ya ci ƙwallaye biyu a ragar Argentina tun a farkon rabin lokaci. Nasarar ta tabbatar da ƙarfin Morocco a gasar, inda ta doke ƙasashe masu ƙarfi irin su Koriya ta Kudu, da Amurka, da Faransa a hanyarta ta zuwa wasan ƙarshe.
- Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Morocco
- Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON
Wannan nasarar ta sanya Morocco zama ƙasa ta farko daga nahiyar Afrika da ta lashe kofin tun bayan nasarar Ghana a shekarar 2009. A ɓangaren Argentina kuwa, rashin nasarar ya kawo ƙarshen burinsu na lashe kofin duniya na matasa karo na bakwai, abin da ya haifar da cece-kuce a ƙasar.
Ko da yake Argentina ta rasa manyan ƴan wasanta biyu — Claudio Echeverri na Bayer Leverkusen da Franco Mastantuono na Real Madrid. Sai dai nasarar Morocco ta jawo murnar gangami a biranen Casablanca, da Rabat da sauran sassan ƙasar, alamar cewa ƙwallon ƙafar Afrika na ƙara samun karɓuwa da daraja a duniya.