Gwamnatin Jihar Gombe, ta ceto yara 59 da ake zargin an yi safararsu cikin watanni takwas da suka gabata.
Daraktan Hukumar Sufurin Gombe Line, Dakta Sani Sabo, ya bayyana cewa nasarar ne sakamakon sabon tsarin sufuri da jihar ta kafa, wanda ya haɗa dukkanin tashoshin mota a waje ɗaya domin samun tsaro mai inganci.
- Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
A cewarsa, haɗin gwiwar da ke tsakanin ‘yansanda, NDLEA, NAPTIP, da NSCDC ta taimaka wajen daƙile manyan laifuka kamar safarar yara, miyagun ƙwayoyi, da makamai ba bisa ƙa’ida ba.
“Mun ceto yara 59 tare da kama miyagun ƙwayoyi da makamai,” in ji Dakta Sabo.
“Yanzu ana rubuta bayanan kowane fasinja da motar da zai hau ta hanyar tsarin rajista na tashar.”
Wasu direbobi sun bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen tabbatar da tsaro, ko da yake fyana jinkirta tafiya.
Wasu kuma sun ce farashin sufuri ya ɗan ƙaru sakamakon sabon tsarin.
Mutane da ƙungiyoyin farar hula sun yaba da nasarar, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa yaran da aka ceto sun samu kulawa, ilimi, da sake gana su da iyayensu.
Dakta Sabo ya ce hukumar sufuri za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro tare da faɗaɗa ayyukanta domin tallafa wa tattalin arziƙin jihar.