Sakaraten gwamnati Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal, ya bukaci shugaban majalisar matasa ta kasa da su kara maida hankali wajen karya guiwa matasa a kan shiga rikice-rikicen siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.
Alhaji Lawal ya nuna bukatar haka a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar majalisar matasan na Jihar Katsina da suka kai masa ziyara a ofishinsa.
Ya bayyana cewa gwamnatin jiha za ta yi duk mai yiyuwa wajen kare nau’in rikice-rikicen siyasa musamman a lokacin gangamin yakin neman zabe don sun sahihin zabe da zai karbu ga al’umma.
Sakataren gwamnati wanda ya bayyana jin dadinsa a kan shirye-shirye daban-daban da kungiyar matasan ta gudanar na wayar da kan matasa kan su guji aikata dabi’u da ba su kamata ba.
Sannan ya yi kira gare su ka da su bayar da dama ga kowane dan siyasa ya yi amfani da su wajen cimma son zuciyarsa.
Alhaji Lawal wanda ya bayyana kungiyar majalisar matasan a matsayin kungiyar da ba ta shiga harkokin siyasa.