Jimilar jami’an kasashe 45 abokan huldar shirye-shiryen dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da na kungiyar Tarayyar Afrika (AU), suna karbar horon dake mayar da hankali kan yaki da talauci, wanda ke gudana a jihar Ningxia ta Hui mai cin gashin kanta daga ranar 19 zuwa 26 ga watan Oktoba.
Yayin horon, mahalarta za su tattauna da masana na jihar da malamai da ‘yan kasuwa da ma’aikata. Shirin wanda ya kunshi jerin lakcoci da ziyarce-ziyarce da shirye-shiryen ilimantarwa da suka shafi kawarwa da rage talauci da hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki da farfado da kauyuka da raya muhalli.
Jihar Ningxia daya ce daga cikin fagagen daga a yakin da Sin ta yi da talauci. Kuma cikin shekarun da suka gabata, kokarin da gwamnatoci a matakan kasa da lardin suka ci gaba da yi, ya kai ga fitar da dukkan kauyukan jihar 1,100 daga kangin talauci. Bugu da kari, daga shekarar 2011 zuwa yanzu, jimilar mutane 803, 000 sun yi adabo da talauci. (Mai fassara: Fa’iza)