A yau Talata ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce an gudanar da bikin kaddamar da kungiyar kasa da kasa ta ayyukan shiga tsakani ko IOMed, a jiya Litinin a yankin Hong Kong na kasar Sin.
Guo Jiakun, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa, inda ya ce IOMed, za ta taka muhimmiyar rawa wajen ingiza gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, ta hanyar bunkasa kiyaye doka, tare da taimakawa yankin Hong Kong ya zama hedkwatar shiga tsakani.
Guo ya ce IOMed, na da nufin bunkasa sassanto, da hadin gwiwa da zaman lumana, da tabbatar da gaskiya, da adalci, da daidaito, kana da ingiza tattaunawa mai zurfi, da hada karfi wajen samar da gudummawar cimma nasara tare, da mayar da hankali ga tsarin da zai dora muhimmanci ga moriyar jama’a da samun nasarori na hakika.
A ranar 30 ga watan Mayun bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar kungiyar IOMed, kuma a madadin kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikinta a yankin musamman na Hong Kong.
Tun daga watan Agustan bana, kasashe 37 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafuwar kungiyar, kana takwas daga cikinsu sun amince da fara aiwatar da ita. A matsayin wadda ta gabatar da shawarar kafa IOMed, kuma mai masaukinta, kasar Sin na kira ga karin kasashe da su gaggauta shiga kungiyar, su kuma shiga a dama da su cikin hadin gwiwar kut-da-kut na ayyukanta, kana su samar da sabuwar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. (Saminu Alhassan)