Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mika kayan agaji cikin gaggawa da kuma magunguna don taimakawa wadanda fashewar tanka ta rutsa da su a ranar Talata a Jihar Neja, wanda ya yi sanadiyyar rayuka sama da 30 tare da jikkata wasu da dama.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na jama’a da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bida/Gbako/Katcha ta jihar Neja, Honarabul Saidu Abdullahi ya gabatar.
Jihar Neja ta fuskanci kalubale na asarar rayuka a ‘yan kwanakin nan, domin tun a ranar 18 ga watan Janairun 2025 wata tankar mai dauke da kimanin lita 60,000 na man fetur ta kife a mahaɗar Dikko dake kusa da Suleja, inda ta kashe mutane sama da 100.
Mummunan lamarin na ranar Talata ya kasance kwatankwacin abin da ya faru a watan Janairu kamar yadda rahotanni suka ce, mutane sun taru a kauyen Essa, suna kwasar mai daga wata tankar mai da ta kife, daga nan kuma sai ta fashe wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 35, da jikkata wasu sama da 40, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.