Rundunar ‘yansandan jihar Gombe a ranar Laraba ta cafke wani yaro dan shekara 15 mai suna Abubakar Aliyu da ke unguwar Tudun Wada Shamaki, bisa zarginsa da aikata laifukan fashi da makami da kuma sata a unguwar Federal Low-Cost da ke cikin birnin Gombe.
Wanda ake zargin, a cewar rundunar ‘yansanda, an kama shi ne biyo bayan wani binciken gaggawa da aka gudanar bayan wani korafin fashi da aka kai a ranar 15 ga Oktoba, 2025.
- Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki
- Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce kamen ya kai ga kwato wasu muhimman kayayyaki da suka hada da iPhone 13 Pro Max, kwamfuta Laptop ta (Apple MacBook), agogo na (Apple), ‘power bank na Oraimo’, da jakar makaranta.
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.
“Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”
Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama wanda ake zargin tare da kwato dukkan kayayyakin da aka sace.