Manzon Allah ya canza tarihin ‘yan Adam duka har ya zuwa abin da muka gani a yau, duk wani abin da yake taruwa cikin jikin duk wani mutum da zai sa ya zama babba, ya cimma burinsa na rayuwa, waɗanna abubuwa sun taru a jikin Manzon Allah (S.A.W.), kamar yadda wannan bawan Allah (masanin falsafa) ya faɗa, ya ce kamar ƙarfin niyya ne (an ce da ka karye a zuciya gara ka karye a ƙafa, domin ƙafa za ta gyaru amma idan zuciya ce ba za ta gyaru ba). A wani wuri da Shehu Ibrahin ke yabon Manzon Allah (S.A.W.) yake cewa “abin da a hankali ba zai yiwu ba, shi Manzon Allah duk ya zo da shi”.
Akwai wani mutum irin mai ji da kansa ɗin nan amma bai yi imani da waliyyai ba duk gaba ɗaya, wasu suka zo za su ƙwace masallaci don sun fi shi karfi, muka haɗu da shi a Madina, ya faɗa min na ce masa ai shikenan tun da ga Sayyada Maryam ta zo ka gaya mata, muka gaisa da ita na ce Sayyada kin ji kin ji, ai ta ce je ka (an gama), wallahi yana zuwa kotu aka ce shi ne da gaskiya, aka cika takardu aka ce idan wancan (mai neman kwace) ya kara magana sai an ɗaure shi, a nan ya kama murna yana cewa ina wannan Sayyadar? Toh haka ake so mutum ya zama mai ƙarfin niyya. Allah ya ji kan Alhaji Garba shi da Hassan suke cewa ba za ka san karamar Shehu Ibrahim ba sai ka taɓo abin da ya fi ƙarfinka. Wannan shine ƙarfin niyya.
- Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
- Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya
Manzon Allah (S.A.W.) yana da ƙarfin niyya, yana da tunani mai zurfi na ƙarshe wanda yake iya gano ƙarshen abin da ake so a gano, wannan gaskiya ce, babu wani Annabi da Allah ya aiko wanda ba shi da hakan. Ahalus-sunnati sun tafi a kan cewa ba a wuridin (neman muƙamin) annabta, za ka iya wuridi ka zama Waliyi, za ka iya cewa ina so na zama waliyi, ina so in zama Gausi, za ka iya yin addu’o’i har Allah ya yaye ma iya abin da ya yaye ma, sai dai wajen Waliyyai suna ganin ka ɗan tawaya saboda ka yi wannan ibadar ce domin wannan abu, amma ba laifi bane in ka yi ma domin zama waliyi, yana da kyau, ba laifi a kan a je kuma a ƙi yi gaba ɗaya.
Ahalus-sunnah sun ce ba a wuridi a zama Annabi, ba wani wuridi da za ka yi ka zama ma’aiki, alal haƙiƙa ni ina ganin hujja kawai an riga an cika, amma da babu abin da babu, ba don Manzon Allah ya cika shi ba, saboda duk Annabawan Allah wuridi suka yi suka haɗu da shi, Annabi Musa (AS) sai da ya yi azumin kwanaki arba’in (40), Manzon Allah (SAW) ma ya zauna a kogon hira, amma mu yanzu zamaninmu; Manzon Allah ya riga ya cika shi.
Babu wani Annabi sai da ya shiga Halwowi ya yi tunani na shekaru da yawa har sai da ya haɗu da haƙiƙanin muradi. Duk ƙwaƙwalwar da take cikin kan mu reshe ne na babbar ƙwaƙwalwa ɗin (aƙalul-a’ala), reshe ne na Manzon Allah (S.A.W.), idan ka iya akwai zikiri da za a ba ka, idan ka yi su ka yi tsarki, ka yi tsarki, in Allah ya yarda reshen yana buɗewa za ka iya haɗuwa da wannan babban (haƙiƙa Muhammadiyya al-aƙalul a’ala). Manzon Allah (SAW) shi ne aƙlul a’ala, sun ce aƙalul-a’ala ɗin nan kamar rumfa yake a kanmu, har wasu sun tafi cewa ita halittar Allah kanta ta azal kamar shape ɗin ƙwaƙwalwa take, sun faɗI gaskiya. Mu kuma Annabi (S.A.W.) shi ya fara tunana mana wannan.
Manzon Allah (S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, tunanin nan har ya shigar da shi duniyar tunani, duniyar tunani ta zamar masa gaskiya har yana tu’ammali da duniyar tunani, in ji mai wannan littafin masanin falsafa. Manzon Allah (S.A.W.) cikin gaskiya ya shiga ya yi tafakkuri, ya ya ibada, ya yi zikiri har ya koma asalinsa har ya haɗu da haƙiƙarsa ta Muhammadiyya (S.A.W.). Wata rana Annabi yana sallah a nan inda yake da Sahabbai, ya ce ga Al’janna ina kallo ga kuma wuta nan ina kallo, kai dai ba ka ji zafinta ba.
Manzon Allah (.S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, yana da yalwar tunani da ƙarfi, kai har abin da ƙwaƙwalwarsa take shirya masa sai ya zama gaskiya, gashi yana gani, in ƙarya ne ya za a yi a gani, a’a wannan gaske ne dama ana haka, kuma mumini a imaninsa idan ya yi imani aljannar nan sai ya ganta tun daga nan duniya, Allah ya kiyaye idan wuta ce sai ya ganta tun a nan, idan mala’iku ne sai ya gan su, duk ba wani abu ba ne zai iya ganin su tun daga nan duniya, ko Annabi ne zai iya ganin shi tun daga nan duniya. Wannan duniyar nan ga baki ɗaya wani ɗigo ne a cikin wannan duniyar ta tunani, ita ma wannan duniyar ta tunani ɗan ɗigo ce a cikin duniyar haƙiƙa.
Mafalsafin nan yake cewa Manzon Allah (S.A.W.) mutum ne mai ɗaukaka da tsarki da ya kai kowane irin matsayi na mai girma (S.A.W.), don haka wata wuya ko wani bala’i bai jin sa, ba wai bai jin sa a haƙiƙa ba ko ya dame shi ba, yana ji amma abin da yake so ya kai ya hana shi jin zafin wannan bala’i.
Manzon Allah yana da ƙarfin hankali wanda ya fi ƙarfin misaltuwa, yana da ƙarfin hankali, sannan yana da ƙarfin haƙuri, abin da zai samu wani gwarzon ya yi raki da ihu, amma Manzon Allah (S.A.W.) sai a yi a gama ba ka san an yi ba. Yana da ƙarfin niyya kamar yadda ya fara faɗa a farko.
Yake cewa ko ka ji an ce yana da wasu abubuwa, ba ana nufin laifi ba ne mai sunan laifi, a’a wani hali ne ya kawo dole ya yi wannan abun, ko kai ne ka zama shugaban jama’a dole ka yi wannan abin, yake cewa dole ce ta kawo, masalaha ce ta kawo kasancewarsa shugaba, kasancewarsa shugaba kuma jagora, ta sa dole sai ya yi wannan, ashe idan da adalci ba za ka kama shi da wannan laifi ba, amma a wajen mai wannan abu laifi ne, ka ga Sayyadina Ali shi ne ya yi irin wannan, ai a yanayin gudanar da mulki dole akwai tsarin da sai an buge shi, ka ga kamar a hukuncin da aka yanke wa Bani Ƙuraiza suka ce a tafi kotun Attaura, wannan hukuncin da ya bi hukuncin Attaura ne, kuma ba Manzon Allah ne ya yi wannan hukunci ba Sa’ad bin Muaz ne ya yi, Manzon Allah (SAW) kuma ya zartar, maslaha ce ta kawo kasancewarshi shugaba, ka ga idan da adalci ba za ka kama shi da wannan ba.
Bafalsafin, yake cewa Manzon Allah (S.A.W.) ya ci nasara wajen zaburar da al’ummarsa, wannan canza al’umma da ya yi, wanna juyi da ya kawo wa al’umma shi ne ya tabbata har yau. Manzon Allah (S.A.W.) bai yi shekara talatin (30) da rasuwa ba sai da mulkin al’ummarsa na larabawa ya kama tun daga Pakistan har ya zuwa Danja, duk mulkinsu ne gaba ɗaya, kuma su mutanen waɗannan wurare duk sun yarda da karatunsa, sun yarda da iliminsa, saboda Allah Ya tsarkake shi, kuma ya sa shi abin bi ne, (S.A.W.) Allah ya tabbatar da ambatonsa a cikin duk wasu shugabanni da aka yi masu tsarki.
Manzon Allah ya taɓa tambayar Jibril (A.S.) me ake nufi da “Wa rafa’ana laka zikirak”sai Jibri (A.S.) ya ce ya tambayo masa, sai ya ce abin da ake nufi shi ne duk lokacin da aka ambaci sunan Allah sai an ambace ka cikin Sallah da cikin ambatonsa da sauransu, saboda (Manzon Allah) ya ƙare cikin Halarar Allah, saboda matsayin da ya kai (S.A.W).
Imamu Zuhuri, (malamin hadisi ne), yana cikn salafus salihin, yake cewa da mutum zai yanka saniya ko ya yanka rago ko kaza da sunan Manzon Allah (S.A.W.) ya halatta a ci, saboda me, saboda Ubangiji ya ce “Wa rafa’ana laka zikirak” ya kawo ambatonsa a wajen, amma in da irin shuwagabanninmu ne na nan sai su ce Haram. Amma sun ce da kirista zai iya yin yanka musulmi ya ci, Allah ya ce abincinsu halal ne a wajenmu, mu ma namu halal ne a wurinsu, sai dai ban da giya da alade da Allah ya haramta (don babu wani abinci na alade da za a kawo ka ci), ka ga bambancin karatun malamai na baya da na yanzu, na baya suna da zurfin tunani.












