Kungiyoyin Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Nijeriya (NULGE) da Kungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT), da Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Nijeriya (MHWUN) sun yabawa Gwamna Uba Sani bisa amincewa da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na kasa tare da karin albashi ga dukkan ma’aikatan kananan hukumomi.
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Kaduna, shugabannin kungiyoyin Kwamared Rayyanu Isyaku Turunku (NULGE), Kwamared Ibrahim Dalhatu (NUT), da Kwamared Umar Ibrahim Fatika (MHWUN) sun bayyana matakin gwamnan a matsayin nuna tausayawa, adalci da jajircewa wajen kare jin daɗin ma’aikata.
- Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano
- Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
Hakazalika, Sun sanar da dakatar da yajin aikin gargadi da suka shirya, bayan gwamnan ya amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga dukkan ma’aikatan kananan hukumomi, ciki har da ma’aikatan da ke ƙarƙashin hukumar ( SUBEB) da Hukumar Kula da Lafiyar a matakin Farko (Primary Healthcare Board), daga watan Oktoba, 2025.
“Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.
Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.
Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta walwalar malamai da iyalansu. Haka kuma sun yaba da gyaran da gwamnati ta yi wajen biyan kudin kungiyoyi da kuma nasarar tantance ma’aikata wanda ya kara gaskiya da tsari a cikin aikin gwamnati.
A fannin lafiya, kungiyoyin sun yaba da sauye-sauyen da Gwamna Uba Sani ya aiwatar, ciki har da farfado da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 255 (PHCs), kafa cibiyoyin kwarewa guda 23 na PHC, da kuma shirin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a duk shekara na tsawon shekaru biyar.
Haka kuma shugabannin ma’aikatan sun jinjina wa gwamnan bisa kaddamar da motocin bas masu aiki da iskar gas (CNG) guda 100 domin bayar da kyautar sufuri ga ma’aikata da dalibai, suna bayyana wannan shiri a matsayin wani mataki na taimakawa wajen rage radadin cire tallafin mai da sauƙaƙa rayuwar jama’a.












