Ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya na ’yan sama jannati, ya ce za a harba kumbon Shenzhou-21 a lokaci mai dacewa a kwanan nan. Yana mai cewa an riga an kai kumbo da rokar da za ta harba kumbon, zuwa wurin harbawa a yau Jumma’a.
A cewar ofishin, an kai kumbon Shenzhou-21 da zai dauki ’yan sama jannati da kuma rokar Long March 2F Yao-21 mai dauke da kumbon zuwa wurin harbawa a yau Jumma’a.
A halin yanzu, kayayyakin aiki a wurin harba kumbon suna cikin kyakkyawan yanayi. Kana za a gudanar da bincike daban daban da kuma gwaje-gwajen hadin gwiwa kamar yadda aka tsara kafin harbawa. Bisa shirin da aka tsara, za a harba kumbon a wani lokaci mai dacewa a nan gaba kadan. (Safiyah Ma)













