A bisa ga abin da aka kira rashin son kai a siyasance, dan majalisar tarayya da ke wakiltar Kebbe/Tambuwal, Honarabul Abdussamad Dasuki ya bayyana cewar ba zai sake tsayawa takarar majalisar wakilai a zaben 2027 ba, matakin da ya dauka na sadaukarwar kashin kai domin bai wa matasa dama.
Dasuki, babban jigo a Majalisar Tarayya, wanda aka fara zabe da shi a majalisar dokoki ta jiha a 2011 ya ce, shawarar da ya yanke ta samo asali ne daga imanin cewar dimokuradiyyar Nijeriya dole ne ta canza domin karbar sabbin muryoyi masu cike da kuzari.
- Gwamnatin Kaduna Tare Da AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma
- Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
“Nijeriyar da muke bukata za ta samu ne kawai ta hanyar sadaukarwa, ya ce “bayan tuntubar jama’a ta, jagoran mu, iyalai na da abu mafi muhimmanci zuciyata, na yanke shawarar ba zan sake tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai a zaben 2027 ba.”
Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.
Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi da matasa a shugabancin kasa.
Yayin da yake waiwayen tafiyar siyasarsa a tsawon shekaru 14 wadda ta hada da Majalisar Dokoki ta Jiha, Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Zartarwa ta Jiha, Dasuki ya bayyana godiya ga mazabarsa, abokan aikinsa, da kuma ubangidan siyasarsa, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Ya ce “Duka babu yadda za a yi wadannan nasarorim su samu ba tare da cikakken goyon baya maras iyaka daga ubangidan siyasa ta ba, kuma jagora na Mai Girma Sanata Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sakkwato)
“Shugaba ne da ya ga baiwa a cikin wani matashi, ya tallafawa burina na siyasa, ya ba ni damar yin hidima a cikin majalisarsa. Har abada zan kasance mai godiya gare shi saboda amincewar da ya nuna a gareni, da kuma damar da ya bani na jagoranci da koyon darussa masu matukar muhimmanci.
“Ga mazaba ta, kun ba ni amincewar ku, kuma na dauke ta a matsayin alamar girmamawa. Ina neman goyon bayanku wajen tabbatar da wannan babban sauyi zuwa sabon babi. Tafiyar da ke gaba ba mai sauki ba ce, za mu fuskanci kalubale da jarrabawa, amma za mu iya shawo kan su idan muka hada kai bisa manufa daya, wato gina Nijeriya mafi kyau, karkashin jagorancin matasa masu kuzari, basira, da kwazo.
“Ga matasa babu wani sauran jira kuma! Babu wani sauran uzuri! Babu sauran shiru! Ku dauki matsayin ku. Ku tsayu da karfi. Ku karbi jagoranci da jarumta da gaskiya da hangen nesa. Ku gina mafi kyawun kyakkyawar makoma.” Ya fada cike da kwarin guiwa.”













