Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa wasu mutane na matsa masa kan ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.
Yayin wani taro da aka gudanar a Jos, Mutfwang ya ce Allah kaɗai da mutanen Jihar Filato ne za su iya yanke hukunci kan makomar siyasarsa.
- APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba
- Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa
“Eh, gaskiya ana matsa min lamba, amma Allah da ku mutanen Filato ne kawai za ku iya sa ni na sauya jam’iyya. Kun taɓa cewa na tafi wani waje?” in ji shi, inda jama’a suka amsa da cewa, “A’a.”
Yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar sauya sheƙarsa, Mutfwang ya ce waɗanda ke yaɗa labarin suna yin hakan ne saboda tsoron tasirinsa.
“Waɗanda ke ƙin amincewa da ni saboda abin da ban faɗa ba suna ɓata lokaci ne kawai,” in ji shi.
“Ko da a jam’iyyar APC akwai mutane da yawa da za su yi farin ciki idan na shiga, amma ba zan shiga ba.”
Ya ƙara da cewa ba zai mayar da hankali kan lamarin ba, inda ya ce, “Wannan labari ne na wani lokaci daban.”














