Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gargaɗi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da hankali a zaɓen gwamnan Anambra da za a gudanar ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
Ribadu, wanda Daraktan Tsaron Cikin Gida, Hassan Abdullahi, ya wakilta a taron tsaro kan zaɓe da aka yi a Abuja, ya ce gwamnati na da cikakken shiri don tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama’a yayin zaɓen.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
- Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
Ya buƙaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su tabbatar da zaman lafiya kafin, yayin da kuma bayan zaɓe.
“Muna aika saƙo mai ƙarfi cewa ba za a yarda da tashin hankali ba,” in ji shi.
Ribadu ya ƙara da cewa hukumomin tsaro za su sanya ido, su ƙara yawan jami’an tsaro, tare da inganta tattara bayanan sirri domin hana duk wani yunƙuri na kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin lumana.














