Mutane biyu, ciki har da ɗan sanda da ɗan hakimi, sun rasa rayukansu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Komi, ƙaramar hukumar Funakaye a Jihar Gombe.
Rikicin ya fara ne a ranar Lahadi bayan wani saɓani tsakanin manoma da makiyaya ya rikiɗe zuwa faɗa, inda matasa daga ƙauyukan maƙwabta suka shiga cikin lamarin.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
- Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
Mohammed Jibrin, mai shekara 27, ɗan Hakimin Komi, ya rasu a asibitin Nafada bayan samun mummunan rauni.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce wani ɗan sanda ma ya mutu bayan wasu matasa, ciki har da waɗanda aka ce daga yankunan maƙwabta suka fito, sun kai wa jami’an tsaro hari lokacin da suka isa wajen don kwantar da tarzoma.
Ya ce mutane 17 aka kama da ake zargi da hannu a rikicin, kuma yanzu an samu zaman lafiya a yankin.
DSP Abdullahi ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike, tare da roƙon mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kuma su taimaka wa ‘yansanda da bayanai.














