Cikin shekaru goma Moderna ta kasance wadda ta kirkiro na’urar da ake amfani da wajen yin tausa ta kimiyyar fasaha RNA (mRNA) da kuma wata allurar data taimaka aka samu saukin samar da magani na allurar cutar Korona.
Amincewar da aka samu wadda ta dauki shekaru a baya, sai aka kammala shi al’amarin cikin watanni, hakan kuwa ta kasance ne ta nasarar da aka samu wajen samar da alluran sinadaran na’urorin mRNA.
Su mRNA da sune ke koya ma sinadaran mutum yadda za su samar da kwayar halittar protein, da ita ma zata taimaka bada kariya ta hana kokarin shigar cuta.
Moderna tana zargin cewar Pfizer yayi amfani ne da fasaharta ta mRNA inda aka kara inganta ta kafin barkewar annobar Korona.
Karar wadda za a shigar da ita ne a kotun Massachusetts da kuma kotun sashe ta Dusseldorf ta kasar Jamus ana bukatar gano da kuma sanin irin asarar kudi da hakan zai jawo kamar yadda, Moderna ta bayyana a jawabin da aka rabawa ‘yan jaridu ranar Juma’a ta makon daya gabata.
Moderna ba zargin cewar Pfizerya yi amfani da fasaharta ta mRNA wadda ta shiga yarjejeniya kanta tsakanin shekarun 2010 da 2016, tun ma kafin bullar annobar Korona a 2019 da har duniya ta san al’amarin tun farkon shekarar 2020 Tun kafin farkon bullar cutar Moderna ta ce ba zata bari ayi amfani da fasharta ba wajen taimakama wasu, sanin yadda za su yi alluransu, musamman ma ga kasashe matsakaita da wadanda suke bi masuTa cigaba da bayanin cewar a watan Maris 2022, ta yi tsammani kamfanoni kamar Pfizer da BioNTech za su mutunta ta wajen damar da take da ita ta fasahar ilimin kimiyya, ta ce ba zata bukaci a biyata wasu kudade ba ga duk abinda aka yi kafin 8 watan Maris 2022.
A sanarwar da aka rabawa manema labarai ta hannunn Moderna ranar Juma’a kamafanin yace Pfizer da BioNTech sun yi amfani da fasaharta nau’i biyu.
Daya ya kunshi sinadarin mRNA kamar dai yadda Moderna ta ce,masana,ma’aikatanta sun fara aikin samar da ita,a 2010,sune kuma na farko da suka da suka fara amfani na gwaji a jikin mutum a shekarar 2015.