Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA, ta ce an shirya harba kumbon Shenzhou-21 da karfe 12 saura mintuna 16 na daren gobe Juma’a, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis, CMSA ta sanar da cewa, ‘yan sama jannati Zhang Lu, da Wu Fei da Zhang Hongzhang, za su kasance cikin kumbon na Shenzhou-21, kuma Zhang Lu ne zai jagoranci tawagar. Dalilan harba kumbon na wannan lokaci su ne kammala sauyin aiki da tawagar ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, da kasancewarsu a tashar sararin samaniya ta Sin na kimanin watanni shida, da gudanar da ayyukan kimiyyar samaniya, da gwaje-gwaje masu nasaba da sai sauransu.
A cewar kakakin CMSA Zhang Jingbo, Sin na rike da kudurinta na sauka kan duniyar wata kafin shekarar 2030, ta kuma tsara jadawalin samar da ci gaba, da gwajin babban aikinta na sauke ‘yan sama jannatinta kan doron wata.
A wani ci gaban, CMSA ta ce ‘yan sama jannati biyu na kasar Pakistan za su samu horo tare da takwarorinsu na Sin, kuma za a zabi daya daga cikinsu don kasancewa tare da kumbon Sin na dakon ‘yan sama jannati na dan wani lokaci a matsayin kwararren jami’i. (Saminu Alhassan)














