Da yammacin yau Jumma’a bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani rubutaccen jawabi mai taken “Ba da gudummawar jagorancin yankin Asiya da Pasific don habaka ci gaban duniya tare”, a gun taron kolin shugabannin masana’antu da kasuwanci na APEC da aka gudanar a Gyeongju dake Koriya ta Kudu.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana cewa halin da ake ciki yanzu a duniya cike yake da sauye-sauye da tashe-tashen hankula, kuma duniya tana tsaye a wani sabon mataki mai muhimmanci, hanyar da za a bi za ta yi tasiri sosai ga duniya. Ya ce ya kamata dukkan bangarorin Asiya da Pasific su sake jaddada burinsu na asali kuma su ba da gudummawa mai kyau ga duniya ta hanyar hadin gwiwa mai karfi da juriya.
Ya yi kira ga kasashen Asiya da Pasific da su jagoranci kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da yin aiki da cudanya da bude kofa da hadin gwiwa mai amfani ga kowa, da kuma bunkasa ci gaba na bai daya mai adalci.
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma)














