Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan furucin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce ya lura da yadda Trump ke ta yin furuci masu tsauri kan Nijeriya, musamman bayan sanya ƙasar cikin jerin “ƙasashen da ake ba su kulawa ta musamman” saboda batun addini.
- Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
- Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci
“Ya kamata a fahimci cewa Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ikon kanta. Matsalolin tsaro da muke fuskanta ba su da alaƙa da addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa. Ɓarayin da ke addabar mu suna cutar da ƴan ƙasa ne ba tare da bambanci ba,” in ji Kwankwaso.
Ya shawarci gwamnatin Amurka da ta daina yin barazana, maimakon haka ta taimaka wa Nijeriya da kayan zamani don magance matsalolin tsaro da ake fama da su.
“Maimakon yin barazana, Amurka ya kamata ta taimaka da kayan aikin zamani don yaƙar matsalolin tsaro, maimakon ƙara raba kan al’umma,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa.
“Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi.
A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai.
“Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso.














