Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki.
A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana za ta kaddamar da matakan soji a Najeriyar.
To sai dai kuma a nata martani, ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar da wata sanarwa, wadda ke musanta zargin na Amurka, tare da jaddada cewa Najeriya na ci gaba da yaki da ayyukan masu tsattsauran ra’ayi, da kare rayukan ’yan kasar, da martaba rayukan mabiya mabambantan addinai da akidu, kana tana biyayya ga dokoki daidai da odar kasa da kasa.
Cikin amsar da ta bayar dangane da tambayar wani dan jarida, Mao Ning ta ce kasar Sin na adawa da wata kasa ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe na daban, ta hanyar fakewa da batun kare hakkokin addini ko na bil’adama. Kazalika, tana adawa da yawaitar barazanar kakaba takunkumai da amfani da karfin tuwo. (Saminu Alhassan)













