Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana wa ‘yan kwangilar da suka yi zanga-zanga cewa Majalisar ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓar bashin cikin gida na Naira tiriliyan 1.15 domin biyan haƙƙoƙinsu.
A ranar Talata, wasu ‘yan kwangila da ba a biya su ba sun rufe ƙofar shiga Majalisar Tarayya, inda suka nuna rashin jin daɗi kan kuɗaɗen ayyukan gwamnati da suka kammala amma ba a biya su ba, lamarin da ya haifar da tsaiko ga ayyukan majalisar.
- Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU
Yayin zaman majalisar, Akpabio ya bayyana cewa an riga an amince da wani ɓangare na bashin cikin gida domin a biya waɗanda suke bi bashi.
Ya roƙi masu zanga-zangar da su yi haƙuri yayin da gwamnati ke kammala tsarin biyan kuɗin.
“Mun amince da bashin cikin gida domin biyan basukan ‘yan kwangila,” in ji Akpabio.
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati.














