Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar’Adua, Janar Mohammed Abdullahi (mai ritaya), ya rasu yana da shekaru 86.
Ya rasu ne da safiyar ranar Laraba.
- Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya
- Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
Ko da yake babu wata sanarwa daga hukumomi dangane da rasuwar, amma Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya fitar da saƙon ta’aziyya.
Marigayin, wanda ɗan asalin garin Ilorin a Jihar Kwara be, za a binne shi ne a maƙabartar ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
A cikin saƙon, Sarkin ya bayyana Abdullahi a matsayin ɗan kishin ƙasa na gari wanda ya yi wa ƙasa hidima a muhimman muƙamai kuma ya taimaka wa marasa galihu.
Ya ce Abdullahi ɗan asalin Ilorin ne mai alfahari da ƙasarsa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa kuma Ya sanya shi cikin Aljannah Firdaus.
An haifi Abdullahi a shekarar 1939, inda ya yi aiki a manyan muƙamai daban-daban a Nijeriya, ciki har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a lokacin mulkin Obasanjo da Yar’Adua.
Ya muma riƙe muƙamin Mai Bai Wa Janar Abdulsalami Abubakar shawara kan harkokin tsaro, Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Ƙasa, da kuma Gwamnan tsohuwar Jihar Benuwe-Filato.














