Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (CFR), ya bayyana shirinsa na kai ƙarar kwamitin yaƙin neman zaɓen Gawuna-Garo bisa zargin cewa shi da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun karɓi cin hancin dala miliyan 10 domin hana tabbatar da naɗin Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC).
Wannan bayani ya fito ne daga Comrade Hafizu Sani Liman, jagoran ƙungiyar All Tinubu/Barau Support Groups, yayin taron manema labarai a Kano ranar Juma’a. Liman ya ce zargin “ƙarya ne, kazafi ne kuma ai yi shi ne da nufin ɓata suna,” tare da ƙara wa da cewa “an ƙirƙire shi ne domin rage darajar Sanata Barau a idon jama’a.”
- Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio
- Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
Jaridar Nigerian Tracker ta rawaito cewa, Liman ya bayyana cewa waɗanda ke da hannu a yaɗa wannan zargi — ciki har da Hon. Muhammadu Badaru Umar da Alwan Hassan — duka ƴan jam’iyyar APC ne, amma sun rungumi siyasar ɓata suna maimakon haɗin kai don cigaban jam’iyyar a Kano. Ya kuma jaddada cewa naɗa shugaban NERC na cikin ikon shugaban ƙasa, ba na Majalisar Dattawa ba.
Ya ƙara da cewa Sanata Barau ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an tantance Engineer Ramat yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa Kwamitin Wutar Lantarki na Majalisa ƙarƙashin Sanata Enyinnaya Abaribe ya kammala tantancewar kuma zai mika rahoto nan ba da jimawa ba.
Liman ya ce lauyoyin Sanata Barau sun samu umarni da su fara shirin kai ƙarar kotu kan masu yaɗa wannan “ƙarya mai hatsari,” yana mai kira ga jama’ar Kano da su yi watsi da zargin. Ya ƙare da cewa Barau “na ci gaba da zama abin koyi ta fuskar gaskiya da aiki tukuru,” tare da nuna cewa “duk wani kazafi ba zai hana shi hidima ga al’ummar Kano da Nijeriya ba.”














