‘Yan’uwa masu bibiyarmu a wannan shafi na Ado Da Kwalliya ina yi muku gaisuwa mafificiya, Assalamu Alaikum.
Ina cikin duba wasu tsofaffin kwafin jaridar Hausa ta wannan Kamfani na LEADERSHIP mai albarka na wasu shekaru da suka gabata, kwatsam na yi kicibis da wani rubutu da Anti Jummai ta taba yi a kan abubuwan mamaki da ake yi da gishiri wajen tsafta da gyara muhalli.
Abin ya yi matukar birge ni da yawa. Wannan ya sa na ce bari mu yi waiwaye adon tafiya da kuma tsarabar wannan mako daga taskar tata kamar haka:
Gishiri yana da amfani da yawa bayan zubawa a cikin abinci, mutane da yawa sun zata amfanin gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma ina, amfaninsa ya fi ga haka.
A wannan ‘yar mukalar uwarigida za ta fahimci cewa gishiri fa abokin tafiyarta ne a cikin dukkanin abubuwan da take yi a cikin gidanta da sauran sirruka na daban.
Daga cikin nazarin da na gudanar, kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa bayan abin da muka sani na al’ada, wato amfanin Gishiri cikin miya, hakikatan sun tabbatar cewa Gishiri dai yana da dimbin sirrika da amfani ga dan adam.
Kan haka ne, na dan zakulo muku kamar haka:
Na farko, kowa ya san cewa idan Kyandir ya diga a waje, tilas zai manne da wajen, har sai an kankare shi da karfin tuwo, amma muddin kika jika Kyandir dinki na tsawon awa biyu ko uku da gishiri, to da zarar kin kunna shi, yana ci, ko da zai diga a waje ba zai kama ba.
Za ki sha mamaki, domin da kin dan murje shi, zai fita, tamkar Kyandir bai taba diga wajen ba.
Abu na biyu, Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi irin na lantarki ko wanda ake amfani da Gas? Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan girkin ko man gyada da kika yi suya da shi, ko dai wani abu da kika dafa a kan risho ya bata shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe, don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce kina saka soso za ki ga ya fita. Haka ma za ki yi wa dukkanin ababen girkinki.
Na uku, idan kina tababar kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a cikin ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya yi kasa, sabanin abin da aka saba gani.
Na hudu, Soson wanke-wanke idan ba a tsaftace, shi sai ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke dabdalarsu a ciki, don haka duk lokacin da ki ka gama wanke-wanke ki wanke soson sosai, sai ki jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko biyu, kuma da zarar kin ga ya fara lalacewa ki yar da shi ki sayi wani, ba wani tsada ne da shi ba.
Abu na biyar, Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade miki, idan kin sayo tsintsiya kafin ki fara amfani da ita sai ki jika ta a cikin ruwan gishiri kafin ki fara amfani da ita.
Ba karshen bayanin ba kenan, za mu ci gaba idan Allah ya kai mu mako mai zuwa.