Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Hajiya Ummi El-Rufai, ta koka da yadda harkar ilimi a Nijeriya ta kara tabarbarewa.
Ta ce Yara ‘yan Makaranta basu samu wadatacce kuma ingattaccen wurin koyon karatu ba.
Da take jawabi a sabuwar makarantar firamare ta zamani da cibiyar Fifth Chukker da access Bank suka gina a Maraban Jos wacce za ta dauki dalibai 12,000 daga yankunan karkara, Ummi wacce ta kasance jakadiyar agaji ta musammam a karkashin kungiyar Majalisar Dinkin duniya UNICEF, ta ce makarantar za ta baiwa yaran karkara damar samun Ilimi mai inganci.
Ta tuna cewa shekarun baya iyayensu sun sami ilimi kyauta kuma mai inganci, sabanin wannan zamani.
Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna ta yaba da shirin gina makarantar firamare da cibiyar Fifth Chukker da Bankin Access suka yi domin amfanar yaran yankin.