Shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na JKS Xi Jinping, ya halarci bikin bude gasar wasanni ta kasar Sin karo na 15 a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong jiya Lahadi.
Lardin Guangdong da yankunan musamman na Sin na Hong Kong da Macau ne suka dauki nauyin gasar. Kuma wannan shi ne karo na farko da yankuna uku suka karbi bakuncin gasar tare.
Gasar ta hada wasanni 34 cikin shirye-shirye 419 da za a fafata. Da kuma wasanni 23 mai shirye shirye 166 da mutane da dama za su shiga a dama da su. Ana sa ran ‘yan wasa 20,000 ne za su fafata a mataki na karshe na gasar.
Gasar ta kasa ita ce irinta mafi girma da ta kunshi wasanni daban-daban, kuma an fara ta ne a shekarar 1959. (Mai fassara: FMM)














