A yau Asabar ne kasar Sin ke gudanar da bikin cika shekaru 77, da cimma nasarar yakin kin harin Japanawa, da yakin nuna adawa da ‘yan mulkin danniya na duniya.
A gundumar Shijingshan dake nan birnin Beijing, jami’an hukuma, da dakarun rundunar ‘yantar da al’umma, da wakilan dalibai, sun yi tattaki zuwa wurin da mahara Japanawa suka kafa tudun harba makamai.
Kaza lika, sun ziyarci daya daga dakarun da suka halarci yakin kin jinin harin Japanawa mai shekaru 97 a duniya, wanda ya ba su wasu labarai game da dauki ba dadin da aka yi, domin dakile harin Japanawa.
A birnin Shanghai kuwa, gwamman Sinawa sun taru, a dakin tunawa na Songhu Kangzhan, wanda aka gina domin tunawa da lokacin barkewar babban yaki a karon farko, domin dakile farmakin dakarun Japan. Jama’ar da suka taru, sun kuma yi shiru na dan lokaci, domin girmama sadaukarwar da ‘yan mazan jiya suka yi domin kare kasar Sin.
Kaza lika a yankin musamman na Hong Kong ma, an gudanar da makamancin wannan biki, wanda ya kunshi buga taken kasa, da daga tutar kasa, da jinjina ga wadanda suka rasa rayukan su, yayin yakin na dakile harin Japanawa, a babban lambun kasa dake birnin, taron da ya samu halartar babban kantoman yankin John Lee, da sauran jami’an sassa, da ‘yan majalissu.
A ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 1945 ne kasar Japan, ta sanya hannu kan takardar mika wuya a yakin duniya na II, kusan makwanni 2 bayan ta ayyana amincewa da hakan.
A shekarar 2014 kuma, kasar Sin ta sanar da ranar 3 ga watan Satumbar ko wace shekara, a matsayin ranar tunawa da cimma nasara kan dakarun kasar Japan. (Saminu Alhassan)