Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC.
Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, da Hon. Sagir Koki, wakilin Kano Municipal.
A cikin wasiƙunsu da Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ya karanta, sun bayyana rikici mai sarƙakiya da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin barin jam’iyyar zuwa APC.
Duk da jayayya da Hon. Kingsley Chinda daga bangaren marasa rinjaye, wanda ya dage wajen ɗaga batun sanarwar a lokacin karanta wasiƙun da karɓar sauya shekarun, Kakakin Majalisar bai amince da buƙatarsa ba.














