Babban Hafsan Sojan Sama (CAS), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya sake jaddada kudirin Rundunar Sojan Sama ta Nijeriya (NAF) na kara kaimi kan hare-haren sama a kan ‘yan ta’adda da kuma dawo da martabar rundunar a idon jama’a.
Aneke ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, NAF na kara kaimi a dukkan ɓangarori don yaƙi da ta’addanci.
- Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
- ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi
Ya bayyana cewa, “Za mu yi duk mai yiwuwa don yaƙar su.”
NAF ta jaddada cewa, rundunar sojin sama ta ci gaba da aiki tukuru, ta himmatu, kuma ta kuduri aniyar mamaye fagen daga da kuma dakile barazanar ta’addanci a duk inda yake.
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojan Sama, Air Cdre Ehimen Ejodame, ya fitar, ta ce CAS ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar aiki da ya kai sansanin rundunar sojin sama na Maiduguri a ranar Litinin, 17 ga Nuwamba, 2025.














