A yau Talata, rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLAN) ta bayyana cewa, babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na yaki na PLANS Fujian ya gudanar da atisayen horaswa na rukunonin dakaru a saman teku, karon farko tun bayan kaddamar da shi.
A yayin atisayen, rukunonin dakarun sun gudanar da horaswa daban-daban, da suka hada da zirga-zirgar jiragen ruwa, da binciken hadin gwiwa da aikin ceto a tsakanin jirgin ruwa da jirgin sama, da tashi da saukar jiragen sama da ake dakonsu a babban jirgin ruwan.
A bangaren aikin bincike da ceto na hadin gwiwa tsakanin jirgin ruwa da na sama, an yi kyakkyawan tsara yadda jiragen ruwa da na sama za su yi hadin gwiwa wajen kammala aikin ceto cikin hanzari, ta hanyar bin umarnin cibiyar dakaru a yayin da ake aikin gaggawa. Atisayen ya taimaka wa habaka kwazon dakarun wajen iya kai dauki kan wani abu da ka iya faruwa ba zato ba tsammani. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














