Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce kalaman da firaministar Japan Sanae Takaichi ta furta dangane da yankin Taiwan na Sin, sam ba su dace ba kuma suna da matukar hadari.
Fu, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin mahawarar shekara-shekara da ake gudanarwa a babban zauren MDD, dangane da sauye-sauye a tsarin gudanar da ayyukan kwamitin tsaron majalisar.
Wakilin na Sin ya kara da cewa, kalaman na Takaichi sun kasance matukar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, da keta manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da hurumin takardun siyasa hudu, wadanda Sin da Japan suka daddale.
Ya ce kalaman nata, sun yi karan-tsaye ga tsarin adalci na kasa da kasa, da odar duniya bayan yakin duniya na biyu, sun kuma sabawa tsarin cudanyar kasashen duniya, tare da shaida kaucewar kasar ta Japan daga alkawarinta na neman ci gaba cikin lumana.
Fu Cong, ya ce kasa irin wannan, sam ba ta cancanci neman kujerar dindindin a kwamitin tsaron MDD ba. (Saminu Alhassan)














