Kalaman katobara da firaministar Japan ta yi sun saba wa dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin dangantakar kasa da kasa, wanda hakan ya tura Japan zuwa matsayin da ta yi hannun riga da al’ummar duniya.
Wani binciken da kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, ta gudanar a tsakanin masu amfani da yanar gizo a sassan duniya, ya nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyinsu galibi sun yi imanin cewa jerin munanan kalamai da ayyukan da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi, wadanda suka hada da zargin tayar da yaki, farfado da ra’ayin nuna karfin soja, da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar duniya, sun cika sharuddan yiwuwar zama “mai aikata laifin yaki.”
Kashi 87.1% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun bukaci Japan da ta janye kalamanta masu tayar da hankali nan take, ta yi tunani sosai kan ayyukanta, sannan ta dauki matakai na zahiri don samun amincewar kasashe makwabta. Bugu da kari, kashi 82.4% na mutanen sun yi imanin cewa ta hanyar la’akari da laifukan da aka tafka a tarihi da kuma kawar da ra’ayin nuna karfin soja ne kawai, Japan za ta iya sake komawa cikin al’ummomin duniya a matsayin wata kasa mai kima yadda ya kamata.
An gudanar da wannan binciken ne a dandalin CGTN na harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, kuma cikin awa 12, masu amfani da yanar gizo 4,549 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu.(Safiyah Ma)














