Uwargidan Shugaban Kasa Nijeriya, Sanata Remi Tinubu, ta yi kira ga amfani da manufofi bisa hujjoji a matsayin babban tsarin dakile cin zarafin yara da yin amfani da su ta hanyar lalata jima’i a duk fadin kasar.
A cikin sakonta na tunawa da Ranar Duniya ta 2025 don Dakile da Warkar da Cin Zarafin Jima’i ga Yara, da ake yi ranar 18 ga Nuwamba, Sanata Tinubu ta ce Nijeriya dole ne ta koma daga “Maganganu da kyawawan niyya” zuwa ayyuka masu ainihi da ke dogara da sahihan bayanai da bincike.
- Ribadu Ya Gana da Sakataren Yaƙin Amurka Kan Iƙirarin Kashe Kiristoci A Nijeriya
- Yunkurin Japan Na Komawa Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ba Zai Yi Nasara Ba
Da taken shekara ta 2025, “Karfafa Kariya ga Yara Daga Cin Zarafi da Lalata Jima’i Ta Hanyar Manufofi Bisa Hujjoji”, Uwargidan Shugaban Kasa ta jaddada cewa kare yara na bukatar shirin da aka tsara da gangan wanda aka gina akan gaskiya, ba zato ba tsammani ba.
Ta bayyana cewa kirkirar muhalli mai bada kariya ga yara Nijeriya na bukatar hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula, shugabannin gargajiya da na addini, iyaye, da matasa.
“A matsayin kasa, dole ne mu tabbatar cewa kowanne yaro ya girma ba tare da tsoro ko hadari ba,” in ji ta, tana rokon duk masu ruwa da tsaki da su sanya kare yara a matsayin babban fifiko na hadin gwiwa.
Uwargidan Shugaban Kasa ta kuma yi addu’a domin tsaron dukkan yara Nijeriya, tana sake tabbatar da jajircewarta ga kokarin kasa na dakile cin zarafi da tallafa wa wadanda suka tsira. “Allah Ya kiyaye dukkan yaranmu,” in ji ta.














