Mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma daraktan ofishin kwamitin kula da harkokin waje na kwamitin kolin, Wang Yi ya gana da mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa na firaministan kasar Burtaniya Jonathan Powell a jiya Juma’a a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana fatansa na ganin Burtaniya ta yi hangen nesa kan dangantakar dake tsakaninta da kasar ta Sin, da kuma daukar ci gaban kasar Sin da zuciya daya, da aiwatar da manufofi masu yakini kan kasar Sin, da kuma yin aiki tare da Sin don cimma buri na bai daya, kana da fuskantar matsaloli kai-tsaye da kuma warware su, da ma dora hadin gwiwar kasashen biyu kan turbar da ta kamata.
Baya ga haka, Wang Yi ya bayyana babban matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Japan, yana mai fatan Burtaniya za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma yin kokari tare da Sin wajen kiyaye nasarorin da aka cimma a yakin duniya na II.
A nasa bangaren, Powell ya jaddada cewa, gwamantin jam’iyyar Labour Party ta kasar Burtaniya tana da niyyar bunkasa dangantaka mai dorewa bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)














