Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, ya shelanta cewa wasu daga cikin jigajigan PDP ne suka taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019.
Sai dai, Wike bai fadi sunayen ‘yan PDP din ba, inda ya ce, manya daga cikin PDP sun kuma same ni don neman goyon bayana amma ban ba su damar yin hakan ba a baya Sabida a wancan lokacin na mayar da hankali ne wajen samun nasarar lashe zaben PDP a Ribas.
Gwamnan ya bayyana hakan a yayin kaddamar da Makarantar Jami’a a yankin Etche da ke a jihar, inda ya kara da cewa, babu wata barazana da wani zai yi masa don ya goyi bayan tafiyar da ya san cewa ba za ta amfani al’ummar jihar sa ba.
Wike ya ci gaba da cewa, in har ba ka gaya min menene jihar Ribas za ta amfana ba, ku manta da ni kawai, domin wannan Gwamnatin Tarayya mai ci, ta yake mu, amma mun rayu, inda ya ce, duk masu surutan nan, idan Gwamnatin ta dira a kansu, dukkanin su sai sun durkushe.
A cewarsa, ni dan jihar Ribas ne, ba bu wani mahaluki da zai iya tsorata ni, inda ya sanar da cewa, wasu mutane sun sheda min cewa, in bi a hankali, za su iya kashe ni, shin wanene ya gaya maka cewa, kai ba za ka mutu ba.