Yau 1 ga watan Disamba, rana ce ta “cutar sida ta duniya” ta 38. Taken aikin fadakarwa a kasar Sin a bana shi ne “Hada kan al’umma don kiyaye gaskiya da kirkire-kirkire, da ma kawo karshen cutar sida.” A kwanan nan, jakadiyar WHO kan rigakafi da shawo kan tarin fuka da ciwon sida Peng Liyuan ta halarci aikin fadakarwa na “Ranar cutar sida ta duniya” ta shekara ta 2025 a cibiyar al’adu ta unguwar Xicheng ta birnin Beijing.
Peng Liyuan ta gabatar da gogewa da fahimtarta na shekaru 20 na aikin fadakarwa kan rigakafi da kula da masu cutar sida, kuma ta karfafa wa mahalarta aikin gwiwa kan yada ra’ayin rigakafin cutar sida, da hada kai tare don ci gaba da kokarin cimma burin shawo kan cutar baki daya. (Mai fassara Bilkisu Xin)














