Ma’aikatar kula da masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta ba da rahoton harkokin da suka shafi manhaja a watanni 10 na farkon na bana, inda aka bayyana cewa, a wadannan watanni 10 da suka gabata, sha’anin manhaja da ba da hidimar sadarwa ya gudana da kyau, kuma kudin shiga a wannan bangare ya wuce kudin Sin yuan triliyan 12.5, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.76. Rahoton ya ce sha’anin na tafiya yadda ya kamata, inda yawan manhajan da Sin ta fitar ke ci gaba da karuwa.
A cikin watannin 10 na farko, yawan kudin shiga na sha’anin manhaja ya kai kudin Sin yuan triliyan 12.5, wanda ya karu da kashi 13.2 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Yawan ribar masana’antar manhaja ta wuce triliyan 1.57, adadin da ya karu da kashi 7.7 cikin 100. Sannan yawan manhajan da Sin ta fitar ya wuce dalar Amurka biliyan 51, wanda ya karu da kashi 6.7 cikin 100, adadin da ya bayyana karuwa a watanni 8 a jere. (Amina Xu)














