A yau 4 ga wannan wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, firaministar kasar Japan Takaichi Sanae ta yi bayanin cewar matsayin kasar Japan kan batun yankin Taiwan ya yi daidai da hadaddiyar sanarwar Sin da Japan da aka cimma a shekarar 1972, kuma lamarin bai sauya ba. Game da ka’idojin da aka bayar bisa tarihi, da zargin da bangaren Sin da bangarorin kasar Japan da ma kasa da kasa suka yi wa kasar Japan, Takaichi Sanae ta ba da amsa ta maganar cewa babu canjawa a matsayin Japan, inda kasar Sin ta ki amincewa da wannan. Sin ta kalubalanci kasar Japan da ta gyara kuskurenta da janye katobarar da Takaichi Sanae ta furta.
A kwanakin baya, sakamakon kuri’ar jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta tsara, domin jin mahangar al’ummun kasa da kasa, ya nuna yadda kaso 91.4 bisa dari suka zargi kasar Japan da kasa nuna matsayi mai dacewa kan batun yankin Taiwan da manufofin ba da kariya ga kasar na musamman, da yunkurin daukar ayyukan soja da sauransu. Mutanen sun yi kira ga Japan da ta dauki alhakinta a matsayin kasar da ta sha kaye a yakin duniya na biyu, da cika alkawarin da ta daukar wa kasar Sin da sauran kasashen duniya baki daya. (Zainab Zhang)














