Ƙungiyar matan jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa (IMMOWA) ta horar da mata da yara sana’o’in dogaro da kai.
Ƙungiyar ta yi bikin bai wa waɗanda suka samu horon takardun shaida a shalkwatan hukumar ta NIS da ke Abuja.
Da take gabatar da jawabi lokacin bikin, Uwargidan shugaban hukumar shige da fita ta ƙasa, Hajiya Maryam Isah Jere ta nuna jin daɗinta bisa samun nasarar horar da mata da yara sana’o’in dogaro da kai tare da ɗora yara a tafarkin tarbiya.
Shugabar ƙungiyar ta ja kunnen waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da abubuwan da suka koya wajen tallafa wa kansu da kuma al’umma gaba ɗaya.
“Ina ƙara wa waɗanda suka amfana da wannan horo ƙwarin gwiwa da su ci gaba da gudanar da sana’o’in da suka koya wajen inganta rayuwarsu.
“Haka kuma ina jinjina ga dukkan waɗanda suka taimaka har aka samu nasarar gudanar da wannan horo. Wannan shirin yana bunƙasa ƙungiyar IMMOWA, wanda yake samun tallafi daga wurin maigidana da sauran jami’ai da ke ƙoƙarin bunƙasa rayuwar mata da yara,” in ji Hajiya Maryam.
Shugabar IMMOWA ta ƙara da cewa maƙasudin wannan shirin shi ne, saboda rashin tsaro da ake fama da shi wanda ya sa yara suna zaune a gida lokacin da iyayansu suke wuraren aiki. Ta ce sun yi tunanin haɗa yaran wuri ɗaya lokacin da iyayensu suke ofis, domin su koyi sana’o’in dogaro da kai.
A cewarta, ta gamsu da irin sakamakon da shirin ya bayar, domin tana ɗaya daga cikin waɗanda suke halartar horon a ko da yaushe tare da mambobin ƙugiyar IMMOWA.
Ta ce wasu daga cikin iyayen yaran suna kiran ta a waya domin nuna godiya da irin tarbiyar da yaran suka samu, inda suka ce a baya yaran ba sa iya gaida kansu, amma a yanzu suna yi. “Sai dai kuma ni ba na buƙatar godiyar mutane, ina neman lada daga wurin Allah.”
Shi ma da yake jawabi, Shugaban hukumar NIS, Isah Idris Jere ya bayyana cewa shirin ƙungiyar IMMOWA ya zo a kan gaɓa ta yadda zai bunƙasa rayuwar jami’ai mata da yaransu.
Wanda ɗaya daga cikin manyan mataimakansa, DCG Dupe Anyalechi ta wakilta a taron, CGI Isah Jere ya ce ƙungiyar ta sauya akalar matan jami’an hukumar ta yadda za su taimaka wa iyalansu da kuma al’umma gaba ɗaya daga abin da suka koya.
Ƙungiyar ta horar da mata da yara yadda ake haɗa sabulu da jaka da burodi da kek da dai sauran kayayyaki da ake amfani da su na yau da kullun.